1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimamin kisan jami'an 'yan sanda

Ramatu Garba Baba
November 1, 2021

Al'ummar kasar Burkina Faso na ci gaba da jimamin kisan da wasu 'yan bindiga suka yi wa wasu jami'an 'yan sanda a yayin wani artabu a tsakaninsu a karshen makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/42QeU
Burkina Faso | Polizeikontrolle
Hoto: Joerg Boethling/imago images

An kai harin ne a yankin arewacin kasar Burkina Faso, inda 'yan sanda biyar suka rasa rayukansu a yayin artabu a tsakanin jami'an 'yan sandan da 'yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata. Sanrwar ma'aikatar tsaron kasar da ke yankin Sahel bayan tabbatar da labarin, ta ce jami'an sun yi nasarar halaka goma sha biyar daga cikin maharan da suka kai harin.

Lamarin ya auku ne a Sourou, yankin Burkinan da ke kusa da kan iyaka da kasar Mali, inda mayakan IS da suka yi kaurin suna, ke kai hare-hare ba kakautawa duk kuwa da kokarin manyan kasashen yamma na kai ma kasashen na Sahel taimako daga hare-haren da suka hana yankin zaman lafiya dama ci gaba. Mutum sama da miliyan daya hare-haren ta'addanci suka raba da muhallinsu a Burkina Faso.