1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shekaru biyar bayan harin ta'addanci a Kano

Nasir Salisu Zango AMA
November 29, 2019

An cika shekaru biyar bayan harin ta'addanci a babban masallacin Juma'a da ke Kano, inda daruruwan mutane suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata wanda har yanzu wasunsu na cikin hali na jinya.

https://p.dw.com/p/3TzSm
Nigeria Anschlag 28.11.2014
Hoto: Reuters

Shekara biyar da wasu mutanen da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da hari a masallacin juma a na fadar Sarkin Kano da ya yi sanadiyar hallaka masallata fiye da 300 tare da jikkata wasu jama'a da dama. Sai dai shekaru biyar bayan kaddamar da wannan harin har yanzu wasu daga cikin wadanda harin ya lahanta na kwance a gida suna jinya bisa rashin kudin aiki ya tilasta musu zama da raunkun cikin yanayi na jiran tsammani.

Mutane da dama a jihar Kano na tuna wannan hari, tare da bayyana shi a matsayin bala'i mafi muni da ya taba faruwa a tarihin Kano, inda a ka shafe tsawon kwanaki ana zaman makoki tare da kokarin kai agaji ga wadanda suke bukatar jinni ko kuma wani taimakon gaggawa ga wadanda suke cikin tagayyara. Masu hannu da shuni da sauran masu mulki da gwamnonin wasu jihohin sun kawo agaji zuwa Kano domin taimakon wadanda hari ya shafa, sai dai duk da hakan har yanzu akwai marasa lafiya dake kwance da  harsashi a jikinsu, wasu rauni ne ke addabarsu inda suke da tsananin bukatar ganin kwararrun likita amma kuma rashin kudin magani yasa dole suke kwance a gida cikin jiran mai afkuwa.

Mutane da dama na cikin mawuyacin hali Muktar Lawal sudawa wani karamin yaro ne da harin ya lalatawa kafa da wasu sassan jiki, har yanzu kafar tasa na cigaba da fitar da mugunyar ruwa amma rashin tsayayyen wanda zai kula da biyan kudin asibiti yasa dole yake kwance a gida cikin tsananin jinya, ya ce" Yana fuskantar tsananin ciyo kuma gashi ciwon yana masa barazanar zuwa makaranta dan haka yake rokon a taimake shi a ceto rayuwarsa." Mahaifan raya da dama sun gaji da zaman jinya a gidajensu duba da rashin isassun kudaden da za su kai yaransu a wasu manyan asibitoci don neman magani, a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakin wadanda suka jikkata a harin ke nuna tsananin damuwa kan batun.

Anschlag Nigeria Kano Bayero Universität
Hoto: REUTERS

A watannin baya an samu tallafin kudade kan batun iftila'in inda har aka taimaki wasu daga cikin marasa lafiyar da ke jinya, to amma sai dai har yanzu da dama na tambayar ko shin kudin sun kare ne ko akwai saura? Gwamnatin jihar Kano har yanzu ba ta mayar da martani ko amsa wannan tambayar ba.