Harin ta′addanci ya hallaka sojoji a Yemen | Labarai | DW | 18.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci ya hallaka sojoji a Yemen

Wani dan kunar bakin wake da ya yi shiga irin ta sojoji, ya tashi bam da ke jikinsa a tsakiyar sojojin da ke kokarin karbar albashi a kusa da barakin Al-Sawlaban da ke birnin Aden.

Da safiyar ranar Lahadin nan wani dan kunar bakin wake da ya yi shiga irin ta soja, ya tashi bam din da ke jikinsa yayin da sojojin suka hallara domin karbar kudadansu na albashi a kusa da barakin Al-Sawlaban da ke unguwar Al-Arish a Arewa maso gabashin birnin Aden.

Sai dai a cewar shugaban ma'aikatar kiwon lafiya na jihar Abdel Nasser Al-Wali wannan adadi na iya karuwa nan gaba. Wannan dai shi ne karo na uku da ake kai wa sojojin na Yemen irin wannan hari kasa da watanni hudu, inda dukanninsu kungiyar IS ta dauki alhakin kai su. A makon da ya gabata ma wani hari irin wannan ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar 48 wadanda suma suka hallara domin karbar albashi.