Harin ta′addanci a kasar Yemen | Labarai | DW | 06.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a kasar Yemen

Kungiyar IS ta dauki alhakin wani harin bam da ya hallaka gwamnan birnin Aden na kasar Yemen Mohammed Saad Jaafar.

Harin kunar bakin waken da ya hallaka gwamnan Aden na kasar Yemen Jafaar Mohammed Saad

Harin kunar bakin waken da ya hallaka gwamnan Aden na kasar Yemen Jafaar Mohammed Saad

Harin bam din dai an kai shi ne a kan ayarin motocin gwamnan yayin da suke wucewa a garin Tawahi da ke kusa da birnin na Aden da sanyin safiyar wannan Lahadin. Aden dai na zama birni na biyu mafi girma a kasar Yemen da ke fama da rikici tsahon watanni, kana a nan ne ma gwamnatin Shugaba Abd-Rabbu Mansur Hadi ke da zama tun bayan da 'yan tawayen Houthi suka kwace iko da babban birnin kasar Sanaa.