Harin ta′addanci a jami′ar Pakistan | Labarai | DW | 20.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a jami'ar Pakistan

Yan sanda kasar sun bayyanan cewa wani Farfesa na daga cikin muta ne 21 da suka mutu bayan harin yan ta'addan wanda aka kai a yankin Peshawar, ko da yake ana ci-gaba da fafatawa don kubutar da dalibai

'Yan ta'addan sun kutsa ne a jami'ar Bacha Khan a birnin Charsadda da ke nesan kilo mita 35 daga Peshawar babban birnin yankin. Maharan sun yi nasarar hawa kan benayen dalibai, abinda ya kawo cikas wajen nasarar kubutar da dalibai cikin lokaci. Yanzu haka dai gidan talabijin din kasar ta Pakistan, ya nuna an kai karin sojoji a inda lamarin ya faru, yayin da ',yan sanda ke cewa sun hallka mayak biyu, amma har yanzu wasu mayakan na saman beni hawa na uku, inda suke ci gaba da musayar wuta da jami'an tsaro. An dai aika da motocin daukar wadanda suka ji rauni, inda ake ci gaba da kai mutane asibiti. Kungiyar Taliban dai ta dau alhakin harin, amma dama can jami'ar Bacha Khan, an rada mata sunan ne, don karrama Bacha Khan wanda ya kaurin suna a sukar kungiyar Taliban.