Harin soji Najeriya ya kashe fararen hula cikin kuskure | Siyasa | DW | 17.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Harin soji Najeriya ya kashe fararen hula cikin kuskure

Manjo Janar Lucky Irabor ya ce harin ya biyo bayan bayanai da suka samu na sake dandazon 'yan Boko Haram a yankin.

 

Wani jirgin rundunar sojin Najeriya  da ke farautar 'yan Boko Haram, cikin kuskure ya kai hari kan bam kan 'yan gudun hijira da jami'an agaji na kasa da kasa. Hatsarin da ya auku a wannan Talatar ya yi sanadiyyar rayukan mutane da yawa tare da raunata wasu.

Kwamandan rundunar sojin da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar Manjo Janar Lucky Irabor, wanda ya sanar wa manema labaru hakan a garin Maiduguri, ya kara da cewar harin ya auku ne a kusa da kan iyakar Kamaru.

Wannan dai shi ne karon farko da rundunar tsaron Najeriyar ta amince da kai hari cikin kuskukre kan fararen hula da jami'an agaji na kasa da kasa.