Harin Saudiya a kan makaranta a Yemen | Labarai | DW | 14.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Saudiya a kan makaranta a Yemen

Saudiya ta ce dakarunta sun kai hari ne a sansanin da mayakan IS ke samun mafaka, amma ta musanta zargin da ake na cewa runduanra sojojin taron dangi da take jagoranta sun kai hari makaranta.

Hare-haren Saudiya a Yemen

Hare-haren Saudiya a Yemen

Rahotanni dai sun nunar da cewa rundunar taron dangin da Saudiyan ke jagoranta a Yemen da nufin yakar 'yan tawayen Houthi, sun kai hari wata makaranta inda suka hallaka wasu dalibai 10 da jiragen yakinsu yayin wani samame ta sama a garin birnin Haydan da ke lardin Saada. Rundunar hadin kan kawancen sun ce indai ba'a yaba da yunkurin lalata bama bamai a sansonin mayakan da ake zargin kasar Iran na marawa baya ba, bai kamata a zarge su da laifin kai hari da ya hallaka dalibaia a wannan makaranta ba. To sai dai kungiyar likitoci na gari na kowa MSF ta tabbatar da cewa jiragen kawancen yakin ne suka kaddamar da hari a kan makarantar.