Harin sama ya salwantar da rayuka a kasar Sudan
December 10, 2025Talla
A Sudan, mutane da dama ne suka rasa rayukansu a daren Talata sakamakon harin jirage marasa matuka da aka kai kusa da babbar cibiyar sarrafa mai ta Heglig.
Rundunar RSF wadda ke fafatawa da sojojin Sudan tun a 2023, ta ce harin ya faru kwana guda bayan ta karbi yankin da ke bakin iyakar Sudan da Kudu.
RSF da sojojin Sudan duka sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba su iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.
Rahotanni daga yankin sun ce akwai shugabannin kabilu da dama da kuma mayakan RSF a cikin wadanda suka rasa rayukan nasu, yayin da Sudan ta Kudu ta ce sojojinta uku su ma sun mutu.
Hukumomi a Sudan ta Kudu sun ce dubban sojojin kasar Sudan sun tsallaka iyaka sun kuma mika wuya.