1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin Lakurawa a Kebbin Najeriya ya kashe mutane sama da 30

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 19, 2026

Sama da shekaru 16 ke nan da arewacin Najeriya ke fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

https://p.dw.com/p/593Ix
Yadda 'yan ta'adda suka kona garin Woro na jihar kwara a Najeriya bayan halaka mutane
Yadda 'yan ta'adda suka kona garin Woro na jihar kwara a Najeriya bayan halaka mutaneHoto: Oluseyi Dasilva/REUTERS

Harin ta'addanci na kungiyar Lakurawa a wasu kauyukan jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya, ya halaka mutane sama da 30, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito.

Rundunar 'yan sandan jihar ta bakin mai magana da yawunta Bashir Usman, ta ce lamarin ya faru a ranar Laraba, inda maharan suka lalata kauyuka bakwai, da suka hada da Mamunu da Awasaka da Tungar Tsoho, sai Makangara da Kanzo da Gorun Naidal da kuma Dan Mai Ago.

Karin bayani - Harin ta'addanci a arewacin Najeriya ya halaka mutane 45

Sama da shekaru 16 ke nan da yankin arewacin Najeriya ke fama da hare-haren ta'addanci, daga kungiyoyin masu ikirarin jihadi, wanda ya faro a yankin arewa maso gabashin kasar, har ya fantsama zuwa sauran sassa.