1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kuskure ya kashe sojojin Afganistan

Abdul-raheem Hassan
October 1, 2017

Akalla jami'an tsaro 10 sun mutu a kasar Afganistan, bayan da sojojin sama suka sako yi subutan bama-bamai a kan dakarun sojin kasa dake aiki a wani shingen bincike da ke kudancin Lardin Heldman a Kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/2l47N
NO FLASH - US Marines in Afghanistan
Hoto: AP

Ma'aikatar tsaron Afganistan dai sun tabatar da aukuwar harin, inda suka ce harin ya faru ne a lokacinda sojojin da ke farautar 'yan tawayen Taliban da ke samun mafaka a yankin da sojojin kasa ke aikin bincike. Wannan harin na zuwa ne bayan da yankin ke ci gaba da fuskantar artabu mai tsanani a tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawayen Taliban.

Harin dai ya faru ne a dai dai lokacin da shugaban kasar Afganistan Ashfar Gani ya gana da hafsan hafsoshin rundunar sojojin kasar Pakistan Janar Qamar Javed Bajwa a birnin Kabul, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi inganta tsaro a tsakanin kasashen biyu da kuma yunkurin farfado da ma'amala a tsakanin juna.