Harin kunar bakin wake ya hallaka rayuka a Borno | Labarai | DW | 29.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake ya hallaka rayuka a Borno

An kwashi mutane da dama zuwa asibiti bayan hari a gaban sansanin 'yan gudun hijira mai mutane sama da 16,000.

Jami’an tsaro da ma'aikatan agaji sun tabbatar da mutuwar mutane tara  inda wasu 21 kuma suka jikkata sanadiyyar tashin wasu tagwayen bama-bamai a bakin sansanin ‘yan gudun hijira da kuma bakin wurin ajiyar mai da ke hanyar Damboa duk a Maiduguri. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan kunar bakin wake da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne suka tashi bama-baman da ke jikinsu da misalin karfe bakwai na safiyar yau din nan. Babban Kwamandan rundunar sojoji ta bakwai Birgediya Janar Victor Ezeogwu ya shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa hare-haren ya yi sandiyyar hallaka mutane 9 tare jikkata wasu mutanen 21. Shi ma shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wacce aka fi sani da NEMA Alhaji Muhamad Kanar ya tabbatar da yawan wadanda suka mutu sanadiyyar tagwayen Bama-Bamai.