1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake aka kai Rasha

April 4, 2017

Gwamnati Rasha tana zargin dan kunar bakin wake dan shekaru 22 daga kasar Kyrgyzstan kan harin bam a jirgin karkashin kasa na birnin St. Petersburg.

https://p.dw.com/p/2agre
Russland Morgen nach dem Terroranschlag in der U-Bahn in St. Petersburg
Hoto: DW/W. Ryabko

Masu bincike a kasar Rasha suna zargin dan kunar bakin wake dan shekaru 22 daga kasar Kyrgyzstan kan harin bam a jirgin karkashin kasa na St. Petersburg birni na biyu mafi girma a kasar. Hukumomin Rasha sun kara kaimin bincike neman bankado wadanda ke da hannu a cikin harin da ya hallaka mutane 14 yayin da wasu kusan 50 suka samu raunika.

An kai harin lokacin da Shugaba Vladimir Putin yake ziyara a birnin na St. Petersburg inda yake ganawa da Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus. Kasashen duniya da dama sun fito fili sun yi tir da halin yayin da manyan kasashe ke cewa za su taimaka cikin binciken da ake yi na neman wadanda suke da hannu a harin na Rasha.