Harin kunar bakin wake a Turkiya | Labarai | DW | 06.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Turkiya

Dan sanda daya ya rasa ransa yayin da wasu biyu kuma suka jikkata a Istanbul babban birnin kasar Turkiya a wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar.

Wata 'yar kunar bakin wake da ba a tantance ba ce dai ta kai hari a ofishin 'yan sanda da ke unguwar Sultan Ahmet. Gwamnan Istanbul Basip Sahin ya tabbatar da mutuwar dan sandan da kuma wacce ta kai harin kunar bakin waken. Tuni dai jami'an tsaro suka killace yankin da aka kai harin da ke kunshe da dimbin jama'a kasancewarsa wajen yawon bude idanu. A nan ne dai Cocin Saint Sophie da kuma Masallacin nan mai tarihi da ake kira da Shudin Masallaci suke.

Mawallafa: Salissou Issa/ Lateefa Mustapha Ja'afar'
Edita: Mohamadou Awal Balarabe