Harin kunar bakin wake a Saudiyya | Labarai | DW | 04.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Saudiyya

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka kansa, ya kuma raunata wasu jami'an tsaro biyu kusa da karamin ofishin jakadancin Amirka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Harin dai ya wakana da daren ranar Lahadi wayewar wannan Litinin, inda dan kunar bakin waken ya ajiye motarsa a gaban wani babban asibiti da ke kallon karamin ofishin jakadancin na Amirka a birnin Jeddah, kuma ya tashi bam din da ke ciki a daidai lokacin da jami'an tsaron biyu suka zo domin bincikensa a cewar wata majiya ta jami'an tsaro. Gidan talbijin din kasar ta Saudiyya ya tabbatar da wannan hari, inda masu bincike ke kokarin tantance gawar wanda ya kai harin.