Harin kunar bakin wake a Iraki | Labarai | DW | 01.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Iraki

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a Iraki ya yi sanadiyyyar rasuwar mutane tara wanda galibisu 'yansanda ne a harabar ofishin karamar hukuma da ke arewacin Tikrit.

Firefighters and Iraqis stand amid the remains of a burnt house after a car bomb that detonated near a Shiite mosque killing three people and injuring 70 others on March 29, 2013 in Kirkuk, 240 kilometers north of Baghdad. A series of car bombs near Shiite mosques targeting worshippers attending weekly prayers killed at least 15 people in the Baghdad neighbourhoods and in Kirkuk city. AFP PHOTO / MARWAN IBRAHIM (Photo credit should read MARWAN IBRAHIM/AFP/Getty Images)

Anschlag auf schiitische Gläubige im Irak

Dan kunar bakin waken dai ya shiga cikin ginin karamar hukumar ne da wata motar dakon man fetur da ya ke tukawa wada ke damfare da bama-bamai inda bai yi wata-wata ba ya tada bam din.

Da ya ke karin haske game da harin, Kyaftin Mohammed Salihi na rundunar 'yansandan Tikrit wanda shi ma ya jikkata a harin, ya ce dan kunar bakin waken ya tada bam din ne lokacin da aka tsaida shi domin yin bincike a daura da ofishin 'yansada da ke cikin harabar.

Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki kai harin. Irin wadannan hare-haren a Iraki dai sun karu tun bayan da yaki tsakin gwamnatin Assad da 'yan tawayen kasar ya ta'azzara.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman