1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Mutane sun mutu a Harin Isra'ila kan Lebanon

April 30, 2026

Hare-haren da Isra'ila ta kai kan kauyuka uku a kudancin Lebanon yayi sanadin mutuwar mutane tara, ciki har da yara biyu da mata biyar, a cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon.

https://p.dw.com/p/5D5KY
Sojojin Lebanon
Sojojin LebanonHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

 Wannan na zuwa ne kusan makonni biyu bayan tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah.

Sanarwar ma'aikatar lafiyar kasar ta kara da cewa, hare-haren Isra'ilan sun kuma yi sanadiyyar jikkata mutane 23, ciki har da yara takwas da mata bakwai.

An fitar da wannan sanarwa ne jim kadan bayan shugaban Lebanon ya soki abin da ya kira ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ke yi.