Harin dakarun Siriya ya yi sanadiyar hallaka kusan mutane 40 | Labarai | DW | 12.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin dakarun Siriya ya yi sanadiyar hallaka kusan mutane 40

Jiragen saman yakin Siriya sun yi barin wuta kan maboyar 'yan aware kusa da birnin Damascus fadar gwamnatin kasar

Jiragen saman yakin Siriya sun yi barin wuta abin da ya kai ga mutuwar kusan mutane 40. Masu raji kare hakkin dan Adam da kafofin yada labaran gwamnati sun tabbatar da faruwar lamarin inda wasu mutane kimanin 120 suka samu raunika. Akwai fararen hula da harin ya ritsa da su, kamar yadda masu kare hakkin dan Adam suka nunar.

Haka na faruwa yayin da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif, yake shirin fara ziyara a kasar ta Siriya. Fiye da 240,000 suka hallaka, yayin da wasu fiye da milyan gudan suka tsere daga gidajensu, tun lokacin da kasar ta Siriya ta fada cikin rudani a shekara ta 2011, sakamakon juyin-juya hali da ya kada a wasu kasashen Larabawa.