Harin bam a kasuwar wayar hannu a Kano | Labarai | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a kasuwar wayar hannu a Kano

Akwai fargabar cewar harin ya ritsa da mutane masu yawa, wanda ke zuwa a daidai lokacin da kasuwar ke cike makil da jama'a.

Jami'an 'yan sanda a kano sun shaidar da cewar an samu tashin bam a kasuwar wayoyin hannu, da aka fi sani da suna Farm Centre. Mai magana sa yawun 'yan sanda Magaji Majiya ya ce tuni aka tura 'yan sanda zuwa kasuwar, a yayin da ake kwasan wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.

Harin na Kano na zuwa ne kasa da awowi 24 da aukuwar na Yola, fadar jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya wanda ya hallaka rayukan mutane 31. Hare haren da ke da alaka da kungiyar nanj ta Boko Haram.