Harin Bam a Kabul | Labarai | DW | 03.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Bam a Kabul

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Kabul na kasar Afghanistan na cewa wani harin Bam ya halaka mutane takwas yayin da wasu 25 kuma suka jikkata.

Harin na kunar bakin wake, an kai shi ne kan ayarin motocin kungiyar tsaro ta NATO da ke dauke da sojojin kasahen waje, kusa da ofishin jakadancin Amirka da ke birnin na Kabul, a dai dai lokacin da ake ribibin safiya ta wannan Laraba.

Bayanani sun ce akwai wasu daga cikin sojoji 'yan kasashen na waje da suka ji raunuka. Harin an kuma kai shi ne kan motocin sulke da aka yi su musamman saboda tserewa manyan hare-hare na nakiyoyi.

Tuni dai kungiyar nan ta IS ta dauki alhakin harin.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Afghanistan ma dai ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ta ce hari ne da aka kai da mota dauke da nakiyoyi.