Harin bam a Jihar Kano | Labarai | DW | 27.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a Jihar Kano

Bayan an kammala sallar Idi lafiya, aka sami rahotanninm hare-hare har biyu, daya a coci, daya a kusa da hanyar shiga babbar jami'ar Kano

A jihar Kanon Najeriya, duk da cewa an gudanar da Idin karamar sallah lami lafiya, an kai wani harin bam a wani Cocni Katholika na Saint Charles da ke unguwar Sabon Gari a wannan Lahadin. Wannan harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar, tare da jikkata wasu guda takwas. Harin ya afku ne bayan da aka tashi Cocin mutane suna kokarin fita dan zuwa gidajen su

Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da afkuwar wannan lamarin, ta bakin kakakinta Frank Mba.

A hannu daya kuma wata mata 'yar kunar bakin wake sanye cikin hijabinta , dake kokarin shiga babbar Jami'ar Kano ita ma a yau Lahadi, ta tarwatsa bam din dake jikin ta, ta kashe kanta, yayin da jami'an tsaro suka gano ta, kuma suke kokorin bincikenta, inda a cewar, kakakin jami'an tsaron 'yan sandar na Najeriya, yar kunan bakin waken ta jikkata 'yan sanda biyar.

Wadannan hare-hare na zuwa ne a yayin da al'ummar Musulmin kasar ta Najeriya ke cikin shagulgullan karamar sallah ta karshen Azumin Ramadan.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Pinado Abdu Waba