Harin bam a Gujba Najeriya | Labarai | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a Gujba Najeriya

Harin ƙunar baƙin wake wanda wata yarinyar ta kai a cikin kasuwa ya hallaka mutane goma.

Harin wanda aka kai a ƙaramar hukumar Gujba da ke cikin jihar Yobe da ke a yanki arewa maso gabashin Najeriyar.Shaidun ganin da ido sun ce wata yarinyar ce ƙarama wace shekarunta ba su wuce 12 ta tayar da bam ɗin a jikinta a tsakiyar kasuwar

A wannan shekara ce Ƙungiyar Boko Haram ta sake karɓe iko da garin na gujba daga cikin hanun dakarun gwamnati.Ya zuwa yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai ana kyautata zaton cewar Ƙungiyar Boko Haram ce ta kai shi