Harin bam a barikin soji da ke Kaduna | Labarai | DW | 25.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a barikin soji da ke Kaduna

Wasu tagwayen hare-haren bam irin na ƙunar bakin wake sun yi sanadiyyar lalata wani coci da ke cikin barikin soji a Jaji kusa da garin Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya dazu.

Harin dai kamar yadda shaidun gani da ido su ka bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi sanadiyyar hallaka mutane goma sha ɗaya.

Baya ga haka tashin bam ɗin ya jikkata masu wake-waken cocin wato 'yan kwaya kamar yadda Mr. DG Haruna Obadia ya yi wa wakilinmu na Kaduna Ibrahima Yakubu ƙarin haske.

Shugabanni a barikin dai sun ce tuni su ka killace duk hanyoyin shige da fice a barikin gami da gudanar da bincike.

Mai magana da yawun shugaban barikin na Jaji da ke ƙaramar hukumar ta Igabin jihar ta Kaduna Bola Koleoso wanda ya tabbatar da faruwar harin ya ce an garzaya da waɗanda su ka jikkata asibitin sojoji domin yi mu su magani.

Jihar Kaduna dai ta sha fama da hare-hare irin na ƙunar baƙin wake wanda a baya 'yan ƙungiyar nan ta Boko Haram su ɗau alhakin kaiwa sai dai kawo yanzu ba wanda ya ɗau alhakin kai wannan hari na barikin sojin na Jaji

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas