Hari ya ritsa da mutane hudu a Maiduguri | Labarai | DW | 12.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya ritsa da mutane hudu a Maiduguri

Shaidu sun bayyana cewar da misalin karfe 11:50 na rana ne wani dan kunar bakin wake da ke tafiya a kan Keke Napep ya tada bam a bakin sakatariyar a birnin Maiduguri.

Rahtanni da ke fitowa daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno sun yi nuni da cewar wani dan kunar bakin wake ya tada bam da ke daure a jikinsa, a bakin sakatariyar jiha inda ake fargabar ya halaka mutane akalla hudu yayin da wasu da dama suka jikkata.

Yanzu haka dai jamian tsaro sun killace wurin da abin ya faru inda ake ci gaba da gudanar ayyukan jin kai. Wani da ya shaida abin da ya faru ya bayyana wa wakilinmu Al-Amin Sulaiman Muhammad ta wayar tarho cewa, tashin bam din ya ritsa da wasu jamian tsaro, inda kuma aka kwashi yawancin wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na Maiduguri.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin awowi 24 da aka samu tashin bam na kunar bakin wake a Maiduguri bayan wani bam da aka nufi wasu masallatai jiya da safe wanda ya halaka mai dauke da shi tare da jikkata masu fita daga masalaci.