Hari ya kashe daruruwa a masallacin Juma′a a Masar | Labarai | DW | 24.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya kashe daruruwa a masallacin Juma'a a Masar

Sama da mutane 230 ne aka tabbatar sun salwanta a wani harin bam da aka kaddamar a masallacin Al Rawdah da ke arewacin Sinai na kasar Masar.

Rahotannin da ke fitowa daga Masar, na cewa sama da mutane 230 ne suka salwanta a wani harin bam da aka kaddamar a masallacin Al Rawdah da ke arewacin Sinai.

Shaidu sun ce 'yan bindigar da suka kai harin sun yi wa masalllacin zobe ne, suka kuma tayar da bama-bamai tare da buda wuta ta hanyar harbe jama'a da bindiga. Kuma baya ga wadanda suka mutun, akwai ma wasu sama da 100 da suka ji rauni. wannan dai shi ne harin ta'addanci mafi muni da aka gani a Masar, wanda aka kai kan masallata a wannan Juma'a.

Tuni kuwa shugaban kasar Abdel Fattah al Sisi, ya gana da jagororin tsaron, jim kadan da faruwar wannan lamari. Shi ma shugaba Donald Trump na Amirka, ya yi tir da harin da aka kai kan masallata. An kuma bayyana kwanaki uku a matsayin na zaman makokin wannan ta'adin. Dama dai sojojin kasar ta Masar na yaki da mayakan kungiyar IS a yankin arewacin na Sinai, yankin da suka kashe Kiristoci da jami'an tsaro da dama.

Ana kuma fargabar samun karuwar alkaluman wadanda za su mutu, saboda irin munin raunuka da mutane suka ji.