Hari ya hallaka fiye da mutane 10 a Najeriya | Labarai | DW | 06.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka fiye da mutane 10 a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da mutuwar wasu mutane fiye da 10 sakamakon wani sabon rikici da ya barke tsakani manoma da makiyaya a Jihar Benue.

Mutane 16 ne suka mutu a sanadiyar sabon rikici da ya barke a tsakanin Fulani makiyaya da wasu matasa a Jihar Benue. Rikicin na kauyen Omutu ya soma ne bayan da Fulanin suka ce an kashe musu 'yan uwa biyu suka kuma dauki matakin kai fansa, daga karshe dai, rayuka fiye da goma ne suka salwanta a yankin da dama ke fama da rikice-rikice masu nasaba da filin kiwo.

Kakakin 'yan sandan yankin Moses Yamu, ya ce an yi wani zaman gaggawa a kokarin kwantar da hankulan al'umma da kuma tabbatar da tsaro a wannan yankin.