Hari ya halaka jami′an tsaro a Libiya | Labarai | DW | 01.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya halaka jami'an tsaro a Libiya

Wani harin Bam da kungiyar mayakan IS ta dauki alhakin kaddamarwa a Libiya, ya halaka dakarun bangaren janar Khalifa Haftar akalla biyu.

Wani harin Bam da kungiyar mayakan IS suka dauki alhakin kaddamarwa a Libiya, ya halaka dakarun bangaren janar Khalifa Haftar akalla biyu a jiya Alhamis, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar. An dai kaddamar da harin a wani wajen binciken ababen hawa dake Nawfiliyya mai tazarar kilomita 80 da wani wajen da ake hakar mai, wajen da manyan cibiyoyin kungiyar kasashe masu hako mai wato OPEC reshen kasar suke.

Rundunar mayakan kasar karkashin Janar Haftar dai na daga cikin manyan mayakan da al'umar Libiya ke ji da ita. Sai dai bangarorin da ke jayayya da rundunar da masu goya masu baya, na takun-saka da ita tun bayan kifar da gwamnatin marigayi shugaba Muamar Gaddafi shekaru shidan da suka gabata.