Hari kan ofishin jakadancin Iran A Yemen | Labarai | DW | 03.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan ofishin jakadancin Iran A Yemen

Wani harin kunar bakin wake da aka kai ya yi sanadin hallaka mutane uku a gida jakadan Iran da ke kasar Yemen, yayin da rahotanni ke cewar wasu karin mutanen sun jikkata.

Harin na yau wanda 'yan kungiyar nan ta Al-Qaida suka dau alhakin kaiwa ya yi sanadin lalata gidan jakadan da ke birnin Sanaa to sai dai jami'an ofishin jakadancin Iran da ke kasar sun ce harin bai rutsa da jakadan ba kasancewar ba ya gidan lokacin da abin ya faru.

To sai dai a wani sako da kungiyar ta Al-Qaida ta sanya a shafin ta na Twitter ta ce harin ya yi sanadin rasuwar jami'an ofishin jakadancin Iran din da damar gaske sabanin ukun da aka hukumomi suka rigaya suka bayyana tun da fari.

Wannan dai ba shi ne karo farko da 'yan Al-Qaida suka kai hari makamancin wannan ba cikin 'yan watannin da suka gabata a kasar ta Yemen wadda suke daukarta da kawarta Iran da ke bin tafarkin Shi'a a matsayin manyan abokan gaba.