1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Filato

February 23, 2026

A kalla mutane 10 ne suka mutu a jihar Filato da ke arewacin Najeriya a wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai yankunan Barikin Ladi da Riyom a daren jiya.

https://p.dw.com/p/59Gqp
Hare-haren 'yan bindiga sun kashe mutane da dama a jihar Filato
Hoto: Oluseyi Dasilva/REUTERS

'Yan bindigar sun kai hare haren ne a yankin Dorawan Babuj da ke karamar hukumar Barikin Ladi, inda suka kashe mutane 9, kafin daga bisani suka shiga kauyen Jol, da ke karamar hukumar Riyom a jihar ta Filato suka kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama. 

Karin bayani: Harin ta'addanci na karuwa a Jihar Filato

A wata ganawa da wakilinmu na jihar Filato, Abdullahi Maidawa Kurgwi ya yi da sakataren watsa labarai na kungiyar matasan Berom ta kasa, Wrang Tengwom ya zargin cewar maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya, bayan kisan wasu Fulani biyar a  karshen mako. A cewar Kurgwi, ya zuwa yanzu hukumomi a jihar Filato ba su ce komai ba dangane da aukuwar lamarin, sai dai wasu  matasa cikin fushi sun toshe babbar hanyar Barkin Ladi, zuwa kudancin jihar Filato don nuna bacin ran su dangane da kashe-kashe da ke aukuwa a yankin.