hare-haren ta´danci a Pakistan | Labarai | DW | 17.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

hare-haren ta´danci a Pakistan

Yankin Waziristan da ke arewancin Pakistan, ya shiga yanayin tashe-tashen hankulla, tun bayan murƙushe yan takifen Jan Massalaci a birnin Islamabad.

A sahiyar yau, a kalla sojojin gwamnati 4 su ka rasa rayuka,a yayin da dama su ka ji raunuka, a sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake da su ka rutsa da wannan yanki.

A tsukin yan kwanaki 3 da su ka wuce, kusan mutane 80 su ka kwanta dama, a cikin wannan tashe-tashen hankulla.

A halin yanzu, mutane da dama na ci gaba da ƙaura daga yankin Waziristan, a sakamakon sanarwar da majalisar Shura ta fiddo, inda ta bayyana kawo ƙarshen yarjejniyar sulhu da ta cimma tare da gwamnati.

A ranar jiya, shugaba Pervez Musharaf ya aika tawagar ta mussamman, da zumar ciwo kan majalisar Shura, ta lashe amen ta , saidai wannan yunƙuri ya ci tura.