Hare-haren kunar bakin wake a Chadi | Labarai | DW | 05.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren kunar bakin wake a Chadi

Rahotanni daga Chadi na cewar wasu hare-hare bam da aka kai sun yi sanadin rasuwar mutane akwalla 27 a wata kasuwa da ke tsibirin Loulou Fou.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na AP cewar baya ga wanda suka rasu din, wasu da suka kai 90 sun samu raunuka, wasunsu ma munana.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda Chadi din a wajen da wannan hari ya wakana ya ce wasu mata ne uku dauke da bama-bamai suka kai harin.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai wannan harin, sai dai kungiyar nan ta Boko Haram ta kai jerin hare-hare a Chadi din don ko a watan jiya ma sai da wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka mutane 3 a wani kauye dab da tafkin Chadi.