1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harbe mutane a Birtaniya

June 3, 2010

An samu gawar mutumin da ya yi ta harbin mutane ba dalili, a yankin dake da masu yawon bude ido

https://p.dw.com/p/NgIB
'Yan sandan BirtaniyaHoto: AP

'Yan sanda a Birtaniya sun samu gawar mutumin da ya harbe mutane 12 a wani yankin dake cike da masu yawon shaƙatawa a yammacin Ingila. Dama dai tun a jiyane 'yan sanda suka ƙaddamar da bincike, don neman direban tasin ɗan shekaru 52 da ya buɗe wuta a tsakiya jama'a. An samu bindigogi biyu a hannun mutumin waɗanda ya yi ta harɓi da su a ƙauyuka masu yawa, kamar yandda shaidun gani da ido suka tabbatar. Wannan shine harbin da yafi kisan mutane a ƙasar Birtaniya tun shekara ta 1996, inda wani ya harbi 'yan makaranta da malamai 16.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissu Madobi