Harbe-harbe sun tsaida jawabin shugaban Burundi | Labarai | DW | 14.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harbe-harbe sun tsaida jawabin shugaban Burundi

A ranar Alhamis din nan ma dai shugaban rundinar sojan kasar Janar Prime Niyongabo ya bayyana cewa yunkurin juyin mulkin ya gaza nasara.

Rahotannin da ke fitowa daga kasar Burundi na nuni da cewa lamura na ci gaba da kazanta, bayan da karar harbe-harben bindigogi suka yi yawa a kusa da hedikwatar yada labarai ta kasar, da tun da fari aka bada rahoton cewa ana musayar wuta tsakanin sojin da ke ikirarin juyin mulki da masu mara baya ga shugaban kasar Pierre Nkurunziza, kamar yadda wanda ya sheda lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

A cewar wanda ya sheda lamarin ya ga soja kwance a mace, kusa da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Burundi.

A wata sanarwa da ta fita ta kafar yada labaran kasar an ji shugaba Nkurunziza ya fara bayanin cewa ya yi Allah wadai da yunkurun yi masa juyin mulki, kuma ya yi afuwa ga duk wanda ya mika wuya cikin wadan nan sojoji, sai dai bayanan shugaban sun katse bayan da aka fara jin karar harbe-harbe.

Manjo Janar Godefroid Niyombare dai ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya tunbuke gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza a lokacin da shugaban ya fice daga kasar. A ranar Alhamis din nan ma dai shugaban rundinar sojan kasar Janar Prime Niyongabo ya bayyana cewa yunkurin juyin mulkin ya gaza nasara.