1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramcin tafiye-tafiye ga masu cin hanci

Ahmed Salisu
October 13, 2018

Gwamnatin Najeriya ta umarci jami'an tsaron kasar da su sanya idanu kana su hana wasu mutane 50 da ake zargi da satar dukiyar kasar ficewa daga Najeriya din har sai an kammala bincike da ma shari'a kan mutanen.

https://p.dw.com/p/36Ump
Karte Nigeria Mubi DEU ENG

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ta fidda a wannan Asabar din ta ce gwamnatin kasar ta dau wannan mataki ne a wani yunkuri na amfani da wata doka da ta bawa shugaban kasar karfin iko na karbe kadarori na wadanda ake zargi da cin hanci a kasar.

Baya ga wannan, dokar har wa yau ta bada dama ta sanya idanu kan hada-hadar kudi da wadannan mutane da ake zargi ke yi don ganin ba su fiddasu zuwa wasu kasashe ba. Ya zuwa yanzu da gwamnatin Najeriya ba ta kai ga bayyana sunayen wadannan mutane ba amma jam'iyyar PDP da ke mulkin kasar ta ce matakin da gwamnatin Buharin ta dauka wani yunkuri ne na kama karya da cuzgunawa wadanda ke jam'iyyun adawa a kasar.