Har yanzu tana kasa tana dabo a Pakistan | Labarai | DW | 10.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu tana kasa tana dabo a Pakistan

Jami´an tsaron Pakistan sun kutsa kai cikin harabar wani fitaccen masallaci dake Islamabad, inda masu tsattsauran ra´ayi na Islama suka mamaye tsawon mako guda. Daukar wannan matakin dai, ya biyo bayan kokarin da jami´an tsaron keyi ne na kubutar da mutanen da ake garkuwa dasu. Jami´an tsaron sun yanke daukar matakin ne bayan da aka gaza cimma sultu, a tsakanin bangarorin biyu .An dai kiyasta cewa daliban masu tsattsauran ra´ayi na garkuwa da mutane kusan dari uku, da yawa yawan su mata da kuma kana nan yara a cikin masallacin. A kalla ya zuwa yanzu mutane 43 ne suka rasu, cikin su kuwa har da soji uku. Mai magana da yawun gwamnatin kasar ya tabbatar da cewa har yanzu, jami´an tsaron na ci gaba da farautar tsagerun, a dai dai lokacin da ake ci gaba da musayar wuta a harabar masallacin a tsakanin bangarorin biyu.