Har yanzu ba a gano sauran ′yan matan da aka sace a Borno ba | Labarai | DW | 18.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ba a gano sauran 'yan matan da aka sace a Borno ba

Ofishin ministan tsaron Najeriya ya sanar cewa ana ci gaba da farautar 'yan bindigar da suka yi garkuwa da 'yan mata kusan 100 na wata sakandare a jihar Borno.

A wasu labaru da ke karo da juna daga Tarayyar Najeriya, ofishin ministan tsaron kasar ya sanar cewa har yanzu ba a samu gano 'yan matan nan kimanin 100 da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka sace su ba.

Shugabar makarantar 'yan matan da ke garin na Chibok inda abun ya faru, ta ce 'yan mata 14 ne kawai suka samu kubuta daga hannun maharan. Sai dai ganin yadda hukumomin tsaron suka nuna gazawarsu kan wannan lamari, a halin yanzu dangin wadanda aka sacen ne suka bazama wajan neman 'ya'yansu a cikin dazuka. A ranar Laraba ce dai rundunar sojojin kasar ta Najeriya ta sanar cewa 'yan mata takwas ne kawai ke hannun maharan, abun da babbar daraktar makarantar da ma hukumomin yankin suka karyata a ranar Alhamis.

Sace 'yan matan dai ya zo ne a daidai lokacin da wani harin bam a kusa da Abuja babban birnin kasar, yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 75, yayin da wasu 141 suka jikkata.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal