Hanyoyin da ake cinikin ma′adinai | Amsoshin takardunku | DW | 26.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Hanyoyin da ake cinikin ma'adinai

Harkokin kasuwancin ma'adanai a kasuwannin duniya, da kasar da ta fi yawan ma'adinai a duniya.

Akwai wadanda aikinsu shi ne dillancin ma'adanai na kasashe zuwa ga kamfanoni masu sarrafa ma'adinan. Dillalai masu lasisi suke sayen ma'adinai na kasashen da aka tono, kuma suke sayar wa ga kamfanoni saboda galibin ma'adinan da ake tono su daga karkashin kasa sai an sake sarrafa su domin mutane su yi amfani da su. Yawanci ana yin wannan harka ta hanyar yin yarjejeniya tsakanin kasshen da suke da ma'adinan da kuma masu saye da sayarwa.

Kasar Rasha a halin yanzu ita ce take kan gaba tsakanin kasashen duniya wajen yawan ma'adinan karkashin kasa, kuma lissafin zai iya sauyawa idan aka kara gano sababbin ma'adinan a wasu wurare na duniya.