Hankali ya kwanta a Burkina Faso | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 21.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Hankali ya kwanta a Burkina Faso

Makonni uku bayan murabus din shugaban kasa Blaise Compaore, 'yan siyasa da sojojin kasar sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya.

Bari mu fara da jaridar Neues Deutschland wadda a babban labarinta mai taken hankali ya kwanta a Burkina Faso ta ce shugabannin siyasa da na sojojin kasar sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya, sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Kimanin makonni uku bayan boren da ya yi awon gaba da gwamnatin shugaba Blaise Compaore, an rantsar da kwararren dan diplomasiyya Michel Kafando a mukaminn shugaban rikon kwaryar kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka. Kafando mai shekaru 72 wanda a lokacin rantsar da shi ya yi alkawarin mutuntawa tare da kare kundin tsarin mulkin kasar, ya ce zai dauki nauyin da aka dora masa da muhimmanci. Kuma yana sane da aikinsa na wakilin al'umma wanda kuma zai jagoranci kasar ya zuwa zabe a badi. A farkon shekaru gommai na 1980 Kafando ya rike mukamin ministan harkokin wajen Burkina Faso sannan daga 1998 zuwa 2011 shi ne jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Burkina Faso. Babban aikin da ke gaban shi yanzu da kuma Firaministan da ya nada shi ne nada wakilai 25 na gwamnatin rikon kwarya.

Galaba a yakin kawar da Ebola

Akwai yiwuwar samun nasara kan cutar Ebola, inji jaridar Die Tageszeitung tana mai nuni da bayanan da gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta bayar cewa an kawar da Ebola daga kasar bayan mutuwar mutane 49 sakamakon wannan cuta. Matakan riga kafi da aka dauka tare da wadanda suka harbu da kwayar cutar ya kai ga samun nasara. A karshen mako ministan kiwon lafiyar Felix Kabange ya ba da wannan albishir a birnin Kinshasa cewa tun ranar 4 ga watan Oktoba wato fiye da kwanaki 42 ba a kara samun wani da ya harbu da kwayar cutar a kasar ba, wato ya ninka har sau biyu wa'adin kamuwa da cutar. Wannan nasarar ya nuna irin muhimmanci da ke akwai idan aka samu cikakken hadin kai tsakanin wadanda abin ya shafa da kuma hukumomin kiwon lafiya, domin Ebola annoba ce da ta shafi kowa da kawo, inji jaridar.

Tsugune ba ta kare ba a Afirka ta Kudu

Rudani ya ki ci ya ki cinyewa a zauren majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu har wayau dai inji jaridar Die Tageszeitung.

Ta ce a mako mai zuwa ma za a fuskanci kace nace a majalisar bayan da a wannan makon shugabar majalisa Baleka Mbete ta sha suka da kakkausan lafazi daga bangaren 'yan adawa, wadanda suka yi fatali da ikon shugabar majalisar, bayan an tura jami'an 'yan sanda cikin majalisar. Dalilin ta da jijiyar wuyan na baya bayan nan shi ne rashin amincewa da yadda jam'iyyar ANC da ma shugaba Jacob Zuma ke tafiyar da mulkin kasar. 'Yan adawa na zarginsa da wani mulki na kama karya da cin hanci da rashawa. Tun a karshen watan Agusta shugaba Zuma ya daina halartar zaman majalisar bayan da 'ya'yan sabuwar jam'iyyar Economic Freedom Fighters suka bukace shi da ya mayar da kudin kasa kimanin Euro miliyan 17 da ya yi amfani da su wajen sabunta gidanshi da ke garinsu.