Halin da ake ciki a Iran | Siyasa | DW | 24.12.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Halin da ake ciki a Iran

Hukumomin na Iran sun haramta gudanar da duk wani taron addu'oi na tunawa da marigayi Ayatollah Hossein Ali Montazeri wanda ya rasu a makon jiya a birnin Qum.

default

Marigayi Ayatollah Hossein Ali Montazeri

A ci gaba da kai ruwa rana da akeyi tsakanin ɓangaren 'yan adawa da kuma hukumomin ƙasar Iran. Hukumomin na Iran sun haramta gudanar da duk wani taron addu'oi na tunawa da marigayi Ayatollah Hossein Ali Montazeri wanda ya rasu a makon jiya a birnin Qum.

A wani rahoto da shafin yanar sadarwar ɓangaren 'yan adawar ƙasar ta Iran suka fitar a yau, sun baiyana cewar hukumomin ta Iran sun ɗauki matakin hana gudanar da adduo'in mako guda da rasuwan Ayatollah Hossein Ali Montazeri ne domin kaucewa duk wata adawa da za'a nunawa gwamnati a lokacin wa'yanan addu'oi kamar dai yadda aka gani a lokacin jana'izan malamin a makon jiya.

Ko'a jiya saida rahotanni suka tabbatar da aukuwar faɗace faɗace tsakanin jami'an tsaro da kuma masu zanga-zanga a garin Isfahan a lokacin da masu adawa da gwamnatin Mahmud Ahmadinejad suke shirye-shiryen gudanar da taron adduo'in tunawa da malamin na Shi'a wanda kuma kafin rasuwar sa yayi ƙaurin suna wajen adawa da gwamnatin ƙasar.

Yanzu dai hukumonin ƙasar ta Iran sunce an haramta duk wani taron addu'oin a sauran yankunan ƙasar, in banda birnin Qum da kuma Najafabad.

A waje ɗaya kuma a yayinda ƙasashen ƙetare keci gaba da yin kira ga gwamnatin ta Iran data sako 'yan adawan da take tsare dasu tun bayan gudanar da zanga-zangar adawa da zaɓen 12 ga watan junin bana da shugaba Mahmud Ahmadinejad ya lashe, wata kotu dake hukunta ɗaruruwan 'yan adawan ƙasar, ta bayyana zartar da hukuncin ɗaurin shekaru shida akan wani ɗan adawa mai suna Abdallah Ramezanzadeh.

Abdallah dai ya kasance tsohon kakakin shugaban 'yan adawan ƙasar Mir Hussain Mousavi ne, wanda kuma aka kama a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a kwanan baya.

A halin da ake ciki da masu zanga-zanga da dama ne dai jami'an tsaron juyin juya halin musuluncin ta Iran suka garƙame tun bayan wancan zanga-zangar adawan, kuma duk da cewar an sako wasu daga cikin 'yan adawan da aka kama, amma har yanzu dai akwai masu adawa da gwamnati kimanin 80 da ake tsare dasu, akasarin su kuma an yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru 15 zuwa sama a gida jarun.

A wannan makone dai ake bikin ashura a ƙasar ta Iran, ranar da kuma take da mahinmanci ga al'umar musulmi musanman mabiya ɗariƙar shi'a, bikin da kuma gwamnati ke fargaban 'yan adawan zasuyi anfa dashi wajen sake nuna adawar su ga gwamnatin Mahmud Ahmadinejad.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Awal