An dade ana ruwa amma kasa na shanyewa game da wawushe arzikin ma'adinai a nahiyar Afirka, to amma ta yaya? Hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba ciniki da kasuwancin ta haramatacciyar hanya na biliyoyin daloli, wanda ke bijirewa hukumomi daga Kongo zuwa Ghana. Su waye kashin bayan wannan ta'asa kuma me ya sa ba za a iya dakile matsalar ba?