Haɗarin jirgin ruwa a Tarayyar Najeriya | Labarai | DW | 29.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haɗarin jirgin ruwa a Tarayyar Najeriya

Rahotanni daga birnin Fatakwal na kudu masu kudancin Najeriya na cewar wasu mutane da yawansu ya kai goma sun rasu bayan da wani jirgin ruwa da suke ciki ya kife.

Wani jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA Onimode Bandele da ya tabbatar da wannan labarin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar suna ta ƙoƙarin ganin sun tsamo sauran mutanen da ba a kai gare su ba.

Mr. Bandele ya ce jirgn ya kife ne bayan da ya tunkuyi wani abu cikin ruwa lokacin da ya ke tafiya. Kifewar jiragen ruwa a Najeriya dai wani abu ne da ake samu daga lokaci zuwa lokaci wanda ake alaƙantawa da yin lodin da ya wuce kima ko gudun wuce sa'a ko ma wata sa'ar rashin ingancin jiragen.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane