Gwamnoni sun nemi daukan matakai kan tsaro | Siyasa | DW | 28.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gwamnoni sun nemi daukan matakai kan tsaro

Tashe-tashen hankula na ci gaba da yi wa Tarayyar Najeriya karan tsaye inda matsalar ke yaduwa zuwa kusan daukacin kasar,.

Alamun rikidewar rikicin rashin tsaron Tarrayar Najeriya ya zama ruwan dare gama duniyar kasar, gwamnonin jihohin kudancin kasar sun ce sun fara fuskantar barazanar maharan da suka kai ga kisan rayuka da dukiya a arewa.

Kama daga Borno ya zuwa Yobe da Adama, sannan daga baya Plateau da Kano da Katsina dama Benue a cikin kasar dai sannu a hankali karamar magana ta zama babba ga Tarrayar Najeriya da ta zauna ta kalli rikicin rashin tsaron kasar har ya zuwa gabar tekun Atlantika da ke kudu.

Wani taron majalisar tattalin arzikin kasar ta Najeriya dai ya ce akalla jihohin kasar 17 fa, yanzu haka na fuskantar barazanar mahara a wani abin da ke sauyin yanayin matsalar da a baya ake yi wa kallon ta jihohi na arewa amma ta gangara har ya zuwa kudancin kasar inda jihohi irinsu Delta da Akwa Ibom da Cross River suka fara nuna alamar atishawar rikicin.

Rahotanni dai a fadar gwamnonin kasar na nuna tururuwa 'yan ina da kisan a cikin manyan motoci da makamai ya zuwa kudu a wani abin da a fadar gwamnan Taraba da ke riko Alhaji Garba Umar ya tada hankali yanzu haka.

“Ana ganin mutanen nan yawanci daga Libiya da Mali da Cadi da kuma Kamaru. Matsala ce da da ake kallon ta arewa amma yanzu ta zama ta ko'ina gwamnonin kudu sun fada mana suna ganin mutanen nan a manyan motoci da makamai, kaga wannan babbar matsala ce da ya kamata a yi maganinta da wuri.” Sabuwar matsalar dai na kara fitowa fili da irin girman kalubalen kasar ta Najeriya da a baya masu mulkinta ke sana'ar siyasa da batun rigingimu, amma kuma ke kallon rushewar rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar.

Abun kuma da ya fara kai ga nunin yatsa ga mahukuntan na Abuja da ke zargin gwamnonin da gazawa wajen iya shawo kan matsalar tun kafin rikidewar ta ya zuwa ga babban rikicin da kasar ke fuskanta ya zuwa haka a cewar Labaran Maku da ke zaman ministan yada labarai kuma kakakin gwamnati

“Jihohi suna da nasu aiki domin tabbatar da zaman lafiya a jihohinsu. Su ne za su shirya masu unguwa, su ne za su shirya sarakuna in sun dauka shugabanci za'a samu zaman lafiya. Amma ka dubi abin da gwamnan Adamawa ya je yana fada a Amirka, ya zauna ya kama jama'arsa a gida babu.” Kokari na siyasa da tsaro ko kuma kokari na gazawa bisa alkawarin karya ga al'umma dai, sabon rikici na kuma fitowa fili da babban matsalar kundin tsarin mulkin kasar da ya kira gwamnonin kasar manyan jami'ai na tabbatar da tsaro a jihohinsu amma kuma a cewar Jonah David Jang da ke zaman gwamnan Jihar Plateau bai basu mallakin soja da 'yan sanda ba.

“Eh mune jami'an tabbatar da zaman lafiya a jihohin mu amma bamu da 'yan sanda ba mu da soja. Suna hannun gwamnatin tarraya. Shi yasa NSA ya ce za'ayi kokari. Muma mun ce a yi kokari a zauna.” Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin rikicin da ya kai ga fitar da sojan kasar daga bariki a kalla jihohin kasar 32 cikin da 36 da nufin kai wa ga bukatar tabbatar da zaman lafiya ga 'yan kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Zainab Mohammed Abubakar/Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin