SiyasaAmurka
Gwamnatin Trump ta yi kiranye ga jakadun kasar 30
December 22, 2025
Talla
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce galibin jakadun sun fara aiki a zamanin tsohuwar gwamnatin Joe Biden. Ma'aikatar ta ce dukkan jakadun da jami'an diflomasiyyar za su dawo birnin Washington DC domin gudanar da wasu ayyukan na daban.
Karin bayani:Sabon matakin diflomasiyyar Trump a Afirka
Kiranyen zai shafi jakadun Amurka a Afirka akalla 13 da suka hadar da na kasashen Burundi, Kamaru, Cape Verde, Gabon, Ivory Coast, Madagascar, Mauritius, Niger, Najeriya, Ruwanda, Senegal, Somalia da kuma Uganda.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Amurka da wasu kasashe irin su China da Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Rasha har ma da Turai ke fuskantar kalubale.