1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Za a yi zabe babu gudu babu ja da baya

Uwais Abubakar Idris
February 20, 2019

Ministan harkokin wajen Najeriya ya  jadada wa  jakadun kasashen waje cewa dole ne a gudanar da zaben kasar a ranar asabar yana mai  cewa gwamnati ba za ta sake lamunta da dage zabe ba.

https://p.dw.com/p/3DkbW
Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Ma'aikatan zabe a NajeriyaHoto: DW/Gänsler

A kokari kwantar da hakulan ‘yan Najeriya da jakadun kasashen waje ministan harkokin wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama ya tabbatar wa kasashen duniya cewar gwamnati ba za ta lamunci sake dage zabe ba, yana mai cewa wajibi ne a gudanar da zaben a ranar asabar ta wannan makon.

’Jakadu da dama sun yi tambayoyi a kan shirin da muka yi kuma hukumar zabe ta ba su amsa, muna murna da irin goyon bayan da suke bamu a kan zaben, muna maraba da masu sa ido a kan zaben kamar yadda suka yi a 2015. Babu irin bayanai na makarkashiya da ba’a yi ba a kan wannan zaben amma babu gudu ba ja da baya dole ne a yi zaben a ranar asabar a ko  wane hali ake ciki“

Wahl Nigeria Abuja
Na'urar zabe card readerHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Tun da farko sai da sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya yi karin haske a kan  matakan tsaro da aka dauka inda ya ce sama da ‘yan sandan Najeriya dubu 300 ne zasu sa ido a kan zaben.

Jakadun kasashen wajen da ke Najeriya dai sun yi tsokaci a kan soke zaben tare da bukatar tabbatar da ganin an gudanar da shi bisa gaskiya da adalci. Suna masu jinjinawa alummar Najeriya da suka nuna son zaman lafiya duk da soke zaben.

Hukumar zaben dai ta ce ya zuwa yanzu ta kammala sake daidaita naurar tantance katin jefa kuria dubu 180,000 Dr Mustapha Muhammad Lecky kwamihsinan ne a hukumar zaben ya bayyana cewa

‘’Mun karbi dukkanin kayan aikin da muke bukata an dubasu, wadanda muka fara rabawa, mun maida su babban bankin Najeriya, yanzu za mu kwashe rarraba su zuwa kananan hkumomi, don haka babu shakka za’a gudanar da zabe a ranar asabar’’.