1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gwamnati ta ce a saki Dasuki da Sowore

December 24, 2019

Gwamnatin Najeriya ta umarci jami'an tsaron kasar da su saki tsohon mashawarcin tsaron kasar Sambo Dasuki da kuma mawallafi na jaridar Sahara Reporters kuma dan siyasa Omoyele Sowore.

https://p.dw.com/p/3VIp1
Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kanal Sambo Dasuki mai ritaya dai ya shafe tsawon shekara hudu yana hannun jami'an tsaron Tarrayar Najeriyar bisa zargin tarka rawa wajen rabo da malaki na Dalar Amirka miliyan dubu biyu da aka ware da nufin sayen makamai na yaki da Boko Haram. Kuma ko bayan nan gwamnatin kasar na zarginshi da mallakar  makamai ba bisa ka'ida ba. To sai dai kuma wasu kotunan kasar sun ba da beli ba daya ba na sakin Dasukin, amma gwamnatin kasar ta yi watsi da umurnin kotunan.

Shi kansa Omoyele Soyere da ke neman kawo sauyi cikin kasar ko ta halin kaka dai ya ji har a kwakwalwa ga gwamnatin da ta kame kuma ta rike shi na tsawon lokaci duk da jeri na zanga-zanga da ma umarnin saki daga  wata kotun Abuja.

Nigeria Omoyele Sowore
Hoto: CC by M. Nanabhay

To sai dai kuma babu zato ba tsammani a wannan Talata 24 ga watan Disemban 2019, gwamnatin kasar ta ba da umurnin sallamar mutanen biyu a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara. Malam Garba Shehu kakakin gwamnatin ya ce matakin sakin mutanen na da nasaba ne da umurnin da kotunan kasar suka bayar a baya. Kafin sakin dai an zargi masu mulkin na Abuja da kin mutunta umarnin kotun musamman bayan kokari na sake kame Sowore a cikin zauren kotu a bangare na jami'an tsaro.To sai dai kuma a fadar kakakin na gwamnati, sakin na mutanen guda biyu ba yana nufin kai karshen jerin shari'un guda Biyu ba.