1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gwamnati ta amince da kasafin kudin 2019

October 25, 2018

A yunkurinta na dorawa bayan fita daga cikin massassarar tattalin arziki, tarrayar  Najeriya tace ta amince da kasafin kudi na Naira Trilliyan  Takwas da Miliyan Dubu dari Bakwai a shekarar 2019.

https://p.dw.com/p/37C9h
Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

Duk da cewar har yanzu tattalin arzikin tarrayar Najeriya bai nuna alamun komawa dai dai ba, akwai alamun karfin gwiwa a bangaren mahukuntan kasar da suka baiyyana kasafin kudin na shekarar badi suka kuma ce akwai alamun tattalin arzikin kasar na ci gaba.

Tarrayar Najeriyar tace zata kashe abun da ya kai Triliyan Takwas da Miliyan Dubu dari bakwai a shekarar badin cikin kasafin da aka gina a bisa hajjar man fetur .

Präsident Buhari und sein stellvertretender Vizepräsident Osinbajo
Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi OsinbajoHoto: Noso Isioro

A cewar ministan kasafin kudi tarrayar Najeriya Udo Udoma kasar na fatan hakar gangar Mai miliyan biyu da dubu dari uku a kusan kullum tare da sai da ita akan dalar Amurka 60 kan kowace ganga a yunkurin kaiwa ga biyan bukata.

A bana dai tarrayar Najeriyar na shirin cin bashin da ya kai na dalar Amurka miliyan dubu biyu da dari tara kafin fatan iya kaiwa ga aiwatar da kasafin dake iya tasiri har ga zabbukan kasar a shekarar badi.

To sai kuma ko bayan bashi wani batun dake barazana ga tattali na arzikin  dai a tunanin mahukuntan na zaman yawan al’umma da haihuwar da bata da tsari. An dai ruwaito ministan kudin kasar Zainab Ahmed tana fadin akwai bukatar sake lale ga yadda ake ta haihuwa ba adadi cikin kasar, abun kuma da tace na shafar daukaci na rayuwar yan kasar da tattali na arzikin al’umma.