1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwashe dalibai daga Arewa maso gabas zuwa wasu jihohi

March 9, 2021

Yayin da gwamnatin Najeriya ta fara aikin kwashe dalibai daga jihohin Arewa maso gabs da nufin mayar da su wasu jihohin saboda yadda satar dalibai a makarantu, masana da iyaye sun fara tofa albarkacin bakinsu.

https://p.dw.com/p/3qP70
Nigeria Hunderte Mädchen in Zamfara entführt
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta fara mayar da daliban ne wadanda yawanci daga sasan jihohin kasar su ke wadanda ke karatu a wasu makarantu na gwamnatin tarayya da ke jihohin saboda tsoron fadawa tarkon 'yan bindiga ko mayakan Boko Haram da ke sace su, suna garkuwa da su don neman kudin fansa ko kuma don a biya musu wasu bukatunsu.

Ana mayar da daliban daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa zuwa jihohin da ake ganin suna da saukin matsalolin tsaro domin magance kokarin sace su don yin garkuwa da su abin da ake ganin ya zama ruwan dare gama duniya musamman a yankunan arewacin Najeriya.

Yaran makaranta lokacin da aka kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Katsina 2020
Yaran makaranta lokacin da aka kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Katsina a 2020Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

To sai dai masana da masharhanta da sauran al'umma na bayyana cewa yin hakan tamkar mika wuya ne ga 'yan ta'adda ko kuma mayar da wasu dalibai zama shafaffu da mai wasu kuma ko oho.

A cewarsu kamata ya yi gwamnati ta yake su, ta hana su sace dalibai a makarantun maimakon sake musu wurare.

A ganinsu mafi hikima shi ne gwamnatin ta samar da tsaro a ko ina ta yadda kowa zai iya zama inda yake ya yi karatu ba tare da samun fargaba ba.

Yanzu haka dai dalibai na makarantun sakandare musamman a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya na zuwa makaranta ne cikin zullumi saboda yadda lamuran tsaro ke kara tabarbarewa, abin da ake gani a matsayin koma baya ga kokarin samar da ilimi ga shiyyar da ke zama ta sahun baya tsakanin takwarorinta na kudancin kasar, in dai a fannin ilimi zamani ne.