1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ladabtar da Rasha kan yunkurin kisan Navalny

Ramatu Garba Baba
March 2, 2021

Gwamnatin Amirka ta kakabawa Rasha takunkumi bayan da ta ce binciken kwakwaf da aka gudanar, ya tabbatar manyan jami'an kasar nada hannu a sanyawa madugun adawa Alexei Navalny guba a abinci.

https://p.dw.com/p/3q71r
Russland | Präsident Wladimir Putin
Hoto: Alexei Nikolsky/AP Photo/picture alliance

A sakamakon da masu binciken a Amirka suka gudanar, sun tabbatarwa duniya cewa, manyan jami'an tsaron kasar shida, sun hada baki a sanya wa Navalny sinadarin Novichok mai saurin kisa, wanda kuma haramtaccen sinadari ne. Gwamnatin Biden dai, ta hada kai da Tarayya Turai da ta riga ta sanya takunkumi kan manyan jami'an gwamnati da ta ce nada hannu dumu-dumu a yunkurin kisan Navalny.

Wannan shi ne karon farko da sabuwar gwamnatin Shugaba Joe Biden ke azawa Rasha takunkumi tun bayan soma jan ragamar mulkin kasar a watan Janairun wannan shekarar ta 2021. Dama gwamnatin Biden ta sha alwashin tunkarar Shugaba Vladimir Putin bisa zarge-zarge na kama 'yan adawa da kusten da kasar ke yi ma kasashen duniya. 

Alexie Navalny ya zame wa gwamnatin Putin karfen kafa, wanda ake ganin a dailin hakan ne aka yi kokarin halaka shi da guba a watan Augustan bara, amma kuma yayi sa'ar tsallake rijiya da baya. An ruga da shi wani asibiti a Jamus inda aka yi masa magani kafin daga bisani ya koma Rasha, amma jim kadan da isa Moscow, aka kama shi tare da yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da rabi.