1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Gangamin neman rage farashin shiga intanet

November 6, 2019

A wani matakin da ke iya kai wa ga kara yawan samun araha ga amfani da intanet a cikin Najeriya, gwamnatin kasar ta nemi ragi bisa farashin damar shiga kafar da kamfanonin sadarwa ke karba yanzu.

https://p.dw.com/p/3SaVg
Wahlen und Smartphone in Nigeria
Hoto: DW/K. Gänsler

Wani kamfen na kafofi na zumunta ne dai ya rikide ya zuwa bukata babba, abun kuma da gwamnatin Najeriya ta ce ya dace a kokari na kara yawan masu amfani da intanet cikin kasar.

Ya zuwa yanzu dai kamfanonin sadarwa na karbar Naira 1000 kan kowane gigabite daya da rabi na damar shiga cikin intanet. Abin kuma da ya mai da shi daya daga cikin kasashe da ke da tsadar damar a nahiyar Afirka.

To sai dai wani umarni na ma'aikatar sadarwa da tattalin arziki na fasaha ta zamani ta umarci daukacin kamfanonin da ke cikin sadarwar da su kara ragi na farashi da nufin kara ba da dama ga 'yan kasar na cin moriyar sadarwa a kasar.

Duk da cewar dai ba ta fadi sabo na farashi ba ministan sadarwa na kasar Dr isa Ali Pantami ya ce wajibi ne ga kamfanonin da su aiwatar da ragin cikin kwanaki biyar domin amfanin 'yan kasar.

Nigeria Smartphone
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Kuma babbar hujjarsa na zaman kara yawan masu amfani da hanyoyin sadarwar da karancin haraji a tsakanin al'umma, abin da ke nufin karin riba ga kamfunan. Shi kansa ministan dai yace ya sha fuskantar 'yar kwange bisa kati na waya da ma damar amfani da intanet a lokaci daban-dabam a baya.

Kamfen din ya mai da hankali bisa tsadar damar ta shiga intanet da ma kwangen katin bugun wayar tsakanin mutane. Aliyu Mudi dai na zaman daya daga cikin yan kamfen da kuma ya ce ragin ya dace a kokari na inganta damar.

Tarrayar Najeriya dai tana fata ragin farashin na iya kai wa ga karin amfanin intanet da kila kara habbaka ga tattalin arzikin kasar.