1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kiki-kaka tsakanin gwamnati da malaman jami'o'i

Uwais Abubakar Idris AMA
November 5, 2020

A Najeriya malaman jami'o'in kasar za su ci gaba da yajin aiki bayan da bangarorin gwamnati da malaman suka sake fuskantar kiki-kaka a yayin tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar ASUU. 

https://p.dw.com/p/3kv8J
Anschlag Nigeria Kano Bayero Universität
Hoto: Reuters

An sake watse baran-baram a tsakanin kungiyar malaman jami’oin Najeriyar da gwamnati inda kowane bangare ke nuna bai fa yar da ba. Abinda ke nuna ci gaba da shan yajin da malaman suka kwashe watani takwas suna yi a kokarin ganin an biya masu bukatunsu. Dr Chris Ngige ministan kwadagon Najeriya yace gwamnati ta yiwa kungiyar malaman jami'o’in tayin basu Naira bilyan 20 ga asusun sake farfado da kayan aiki a jami’o'i a matsayin nuna da gaske take kan alkawarin da suka cimawa da kungiyar a 2013 inda yace "Mun nuna da gaske muke bama adawa da wannan, to amma fa saboda halin tattalin arziki ba zamu iya biyansu Naira bilyan 110 da suke nema ba shi yasa muka yi masu tayin Naira bilyan 20."  Muhimmin batun da ake takadama a kansa shine na sai malaman jami'o'in su shiga tsarin biyan albashi na bai daya watau IPPS da gwamnatin tace sai ta gwada manhajarsu don sanin igancinta, amma batun biyansu sauran hakokinsu a yanzu dole sai ta wancan tsari. An kwashe watanni 10 ba tare da karatu a jami'o'in kasar lamarin da ya haifar da babbar illa ga tsarin karatun Najeriya a cewar Dr Hussaini Tukur malami a jami’ar jihar Nasarawa. Malaman jami'o’in Najeriyar na kan gaba wajen yawan yaje-yaje aiki abinda ke shafar daukacin tsarin ilimi tare da haddasa rudanin rayuwa ga dalibi domin yana da wahala ya san ko har yaushe zai kamala karatunsa lamarin da ya sanya iyaye na neman mafita kan tabarbacewar ilimin yara baya ga tururuwa zuwa jami'oi masu zaman kansu amma ga wadanda suka mallaki abin hannusu don yin haka.