Gwamnan Sokoto ya koma adawa a Najeriya | Labarai | DW | 01.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnan Sokoto ya koma adawa a Najeriya

Gwamnan jihar Sokoto a arewacin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP da ke adawa.

Gwamnan na Sokoto wanda ya yi kaura suna wajen goyon bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhar ya sanar da sauya shekarsa gaban daruruwan magoya bayansa a jihar ta Sokoto.

Gwamna Tambuwal da a baya ya rike shugaban majalisar wakilai a tarayya ya sake bin sahun 'yan uwansa da suka yi kaura daga jam'iyyar PDP gabannn zaben 2015 da ya kai Buhari kan mulki, inda suka sake komawa inda suka fito. Sai dai a cewar Tambuwal ra'ayin al'ummar Sokoto ya sa shi daukar wannan mataki.

Ana dai rade-radin cewa shi ma Tambuwal na daga cikin masu muradi na kai wa ga kujerar shugabancin na Najeriya sai dai bai kai ga bayyanawa ba.